An kone gidajen wasu ko rufi babu. Cikin gidajen irin mutanen da aka bari a bayan sun kone sai tokarsu. Wasu gidajen kuma an balle kofofin su an sace kayan dake ciki da suka hada da kayan abinci da tukwane.
Ma’aikatan agaji na gargadin cewa kasar na komawa cikin rikici. Kimanin mutane 100,000 sun gudu sun bar gidajen su tun watan Satumba.
A Arewa, yankin da yake da mafi yawan Kiristoci, ‘Yan tawayen Anti-Balaka sunyi amfani da kauyen Bambara a matsayin mazaunin su. Amma bayan sojojin sun sace shanu daga hannun makiyayan da ke makwabtaka dasu, tsofaffin Yan bangar tsoffin ‘yan Seleka suka je ramuwar gayya, inda suka kashe mutane kimanin 25 suka kuma kona gidaje fiye da 600.
Facebook Forum