Wani rahoto da Kungiyar dake kula da harkokin teku da jiragen ruwa ta bayar ya nuna cewar, raguwar kula ko kuma sa ido na ba ‘yan fashin teku damar baje kolin kai hare hare akan jiragen dake zirga zirga a kusa da gabar tekun Somaliya.
Rahoton da wata kungiya mai zaman kanta da ake kira da “Oceans Beyond Piracy” ta bayar yace bayan an yi shekaru masu yawa ba’a ga irin wannan fashin na teku ba, yawan jiragen ruwan da ke zuwa bakin gabar ya ragu, kamar yadda yawan jami’an tsaro na ruwa masu zirga zirga a kusa da Somaliya shima ya ragu.
Maisie Pigeon, wadda ta jagoranci rubuta rahoton ta ce, “daya daga cikin abubuwan da muka gano shine cewa daman barayin basa taba yin nisa da gabar tekun Somalia, kuma suna cigaba da zama cikin shiri da kuma mallakar kayan aikin da zasu iya cigaba da wannan ta’asar tasu.”
Akalla hudu daga cikin jiragen ruwa bakwai da aka kaiwa hari a wannan shekarar basa dauke da jami’an tsaro da makamai a cikinsu.
Facebook Forum