Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, shine ya bayyana hakan a wata takarda da ya rabawa manema labarai a babban birnin Abuja. Wani mataki da tsohon shugaban hukumar kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai Abdulmumini Jibrin, yace shine ya shigar da kara akan shugabannin Majalisar su 13.
A cewar Jibrin, anyi kokarin tilasta masa da ya shigar da ayyuka da suka kai adadin kudinsu ya kai Biliyan 30, wanda yanzu haka ya hada takardun shaida ya mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ya kuma yi ikirarin cewa idan har ba a dauki mataki mai tsanani ga wadanda ake zargi ba to tabbas magana zata kai ga har kotun duniya.
A wani abu mai kamar mayar da martani ‘daya cikin wadanda ake zargi da taba kasafin kudin, kuma gagabadan Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa, yace babu wani abu da za a iya yi a kasafin kudin a halin yanzu. Inda yace akwai doka da akayi ta cikin gida wadda ta baiwa ‘yan Majalisa ikon tsara wani abu da suka yarda da shi don gudanar da aikinsu.
Domin karin bayani saurari rahotan Madina Dauda.