Shugaban kungiyar na shiyyar A dake yankin arewa maso yammacin Najeriya da jihohi 8 a karkashinta,Comrade Kabir Yunusa ne yayiwa manema labaru wannan jawabi akan wannan matasaya a wani taro da kungiyar ta kira a garin Kaduna.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa a shekarar 2013, da 14, ‘ya’yan kungiyar sun yi yajin aiki na kusan watanni 9, akan wasu bukatoci da suka gabatarwa gwamnati wadanda har yanzu basu cimma matsaya a game dasu ba, kuma da alamun gwamnati bata da niyyar duba lamarin.
Ya kara da cewa abin takaicin shine suna cikin fama da wadannan matsaloli kuma sai ga wata sabuwa ta kunno kai, wato rashin biyan wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar albashin su, wasu kuma rabi suke samu kana wasu kuma basa samun alawus alawus dinsu tun daga watan daya na wannan shekara da muke ciki.
Daga karshe ya bayyana cewa babban makasudin kiran waannan taro nasu shine domin su sake jaddadawa gwamnati cewar lallai sun bata daga yanzu zuwa ranar ashirin da daya ga wannan wata na agusta, idan bata yi masu wani abu ba, babu shakka zasu tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.
Idan ba’a manta ba kungiyar ta yi barazanar shiga yajin aiki a farkon shigowar sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kafin ta janye yunkurin da kanta domin ba gwamnatin uzuri.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.