Kasancewar an cimma matsaya kan canjin dalar zai kasance bisa yadda farashin yak e a kasuwa a wanncan lokaci wato Naira dari da tasa’in da bakwai akan dala daya. Hukumar aikin hajji ta kasa ta sanar da hukumomin alhazai na jihohi, su kuma suka sanar da maniyyata, maniyyatan kuma suka biya kudaden su ga hukumomin alhazai na jihohi, kana aka tura kudaden Abuja.
Ya kara da cewa yanzu basu da hujjar komawa su fadawa alhazan cewar su sake biyan wani adadin da bashi akayi alkawari tun farko ba.
Malam Yusha’u Aliyu, kwararre ne akan harkokin tattalin arziki a Najeriya kuma yayi Karin bayanin cewa hukumomin aikin hajji wuri ne inda mutane ke iya aje kudi har na tsawon shekara guda, kuma ana ajiye ka’idojin yadda za’a gudanar da duk hada hadar.
Hakan na kasancewa ne a matsayin madafar da maniyyata suke da ita domin kuwa sun bada kudaden su, sa’an nan kuma hukuma ke a madadin su.
Yanzu dai farashin dalar yah aura Naira dari uku, yayinda kasuwar bayan fag eke dab da Naira dari hudu, amma babban bankin Nageriyar y ace za’a canzawa maniyyata aikin hajjin akan Naira dari da tasa’in da bakwai.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.