Gwamnatin tarayyar ta ce an samu bullar cutar ne a kananan hukumomin Gwoza da Jere da ke jihar ta Borno.
Hakan na faruwa ne shekaru biyu bayan da Najeriya ta kwashe ba tare da sake samun bullar cutar ba a duk fadin kasar.
Cutar shan inna kan haifar da nakasa ga yara kanana ko a kafa ko kuma a hanu, lamarin da kan kai ga su rika tafiya da sanduna.
Yanzu haka gwamnatin tarayya ta aike da kwararru a fannin kiwon lafiya tare da hadin gwiwar jami’an gwamnatin Borno domin a dakile yaduwar cutar.
Bayanai sun yi nuni da cewa dubban yara za a yiwa alluran rigakafi a duk fadin jihar ta Borno, a matsayin wani mataki na kaucewa bazuwar cutar.
Domin jin cikakken bayani dangane da wannan lamari, Sahabu Imam Aliyu ya zanta da kwamishinan Lafiya na jihar ta Borno, Dr. Haruna Mshelia, inda da farko ya nemi karin bayani dangane da lamarin: