Tsohon ministan harkokin cikin gida Mohamed Bazoum, dan takarar jami’iya mai mulki, shine wanda shugaban kasa Mahamadou Issoufou yake goya masa baya, shugaban wanda ke kammala wa’adinsa na biyu na shekaru biyar da ya kwashe yana mulkin kasar mai yawan sahara da kuma yawan al’umma miliyan 23.
Bazoum mai shekaru 60, ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan shugaba Issoufou, yayin da ya lashi takobin yakar batun cin hanci da rashawa.
Ya ce “idan na yi nasara aka zabe ni, lallai kun zabi mutumin da ya yi shiri tun daga ranar farko da zai kama aiki,” yana fada a wani gangamin yakin neman zabe ta hoton bidito.
Jamhuriyar ta sha fama da haren hare a kusa da iyakarta da kasashen Mali da Burkina Faso daga ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyoyin al-Qaida da IS.
Haka zalika iyakokinta da Najeriya a kudancin kasar ke huskantar hare haren kungiyar Boko Haram.
An kashe daruruwan sojoji da fararen hula a shekarar da ta gabata kadai.
Sama da kashi 40 cikin 100 na al’ummar kasar ke rayuwa cikin tsananin talauci kana annobar COVID-19 kuma ta yiwa tattalin arzikin kasar illa kamar kasashe da dama a duniya, haka zalika batun canjin yanayi da fadiwar farashin karfen yuraniyam a kasuwar duniya suka yi mummunar tasiri a kan tattalin arzikin kasar.
Bazoum zai fafata ne da ‘yan takara 29, karawar da ake ganin ka iya kai ga zagaye na biyu idan sun hana masa samun kuru’u masu rinjayi.
Hama Amadou da ya zo na biyu a zabe na baya, an dakatar da shi daga shiga takarar zabe saboda hukuncin aikata laifi da aka taba yanke masa, lamarin da yasa babbar jami’iyar adawa ta rasa dan takara.
Amma a makon da ya gabata, jami’iyar Amadou ta kira magoya bayanta da su bada kuru’unsu ga Mahamane Ousmane wanda ya taba shugabancin kasar daga shekarar 1993 zuwa 1996.