Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga Watan Ramadan A Saudiyya


Watan azumi a kasar Lebanon
Watan azumi a kasar Lebanon

Jami'ai sun ce anga jinjirin wata a daren Lahadi a kasar Saudiyya, inda ake da wurare mafi tsarki a addinin Musulunci, wanda ke nuna yadda za a fara azumin watan Ramadan ga da yawa daga cikin musulmi biliyan 1.8 na duniya.

Watan Ramadan mai alfarma, wanda masu ibada ke kiyaye abinci da ruwa daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, yana nuna lokacin yin ayyukan addini, da haduwar dangi da bayar da kyauta a fadin duniyar musulmi. Ganin wata a daren Lahadi yana nufin Litinin ita ce ranar farko ta azumi.

Tashar talabijin ta Saudiyya ta rawaito mahukuntan kasar sun ga jinjirin wata. Ba da jimawa ba, kasashen Larabawa da dama na yankin Gulf, da Iraki da Siriya, sun bi sanarwar don tabbatar da cewa su ma za su fara azumi ranar Litinin. Shugabannin sun kuma yi ta musayar sakonnin taya murna cewa an fara watan azumi.

Sai dai akwai wasu kasashen Asiya da tekun Pasifik kamar Australia da Brunei da Indonesia da Malaysia da kuma Singapore, da za a fara azumin watan Ramadan a ranar Talata bayan kasa ganin jinjirin watan. Oman, da ke gefen gabas na yankin Larabawa, ta kuma sanar da cewa za a fara azumin watan Ramadan ranar Talata. Kasar Jordan itama za ta fara azumin watan Ramadan a ranar Talata.

Azumin watan Ramadan na bana ya zo ne a daidai lokacin da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ruruwa sakamakon yakin da Isra'ila da Hamas ke ci gaba da yi a zirin Gaza. Hakan ya haifar da fargabar cewa rikicin na iya haifar da tarzoma fiye da iyakokin da ake fama da su a yanzu.

Sarkin Saudiyya Salman ya yi nuni da yakin Isra’ila da Hamas a wasu kalamai da aka yi wa jama’a bayan sanarwar watan Ramadan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG