Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Ta NLC Ba Ta Yi Armashi Ba A Arewa Maso Yammacin Najeriya


Mambobin NLC a jihar Kano
Mambobin NLC a jihar Kano

Rahotanni daga shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na nuni da cewa, zanga zangar lumana da kungiyar kwadagon kasar ta gudanar a yau ba tayi armashi ba, musamman a jihohin Kano da Jigawa, Katsina, Kebbi da kuma Zamfara.

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ce ta umarci rassan jihohi 36 na gamayyar kungiyoyin kwadago dake karkashinta su fita zanga zangar lumanar domin nunawa gwamnati damuwar kan halin da ‘yan kasa ke ciki na yanayin tsadar rayuwa da kuma rashin tsaro a sassan kasar.

Mambobin Kungiyar Kwadago A Jihar Kano
Mambobin Kungiyar Kwadago A Jihar Kano

A jihar Kano, ‘yan kwadagon sunyi tattaki zuwa gidan gwamnati karkashin jagorancin shugaban su Kwamred Kabiru Inuwa.

Kwamred Maimuna Garba, mataimakiyar shugaban kungiyar kwadagon ta NLC reshen jihar Kano tace “gwamnatin nan kafin ta hau mulki ta yiwa ‘yan kasa alkawurra da dama, da suka hada da samar da ayyukan yi ga matasa, za ta saukakawa talaka rayuwa zata bude hanyoyin kasuwanci, amma yanzu gashi mutane suna fama da yunwa da fatara”

Mambobin kungiyar Kwadagao ta NLC a jihar Kano
Mambobin kungiyar Kwadagao ta NLC a jihar Kano

Shugaban ma’aikatan gwamnati Abdullahi Musa ya karbe su a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf, inda yace gwamnati na nan tana tsare-tsaren saukakawa mutane rayuwa, musamman la’akari da karatowar watan Ramadan.

A jihar Jigawa kuwa ‘yan kwadagon ba su kai ga mika sakon su ba ga gwamnatin jihar, al’amarin da wasu ke alakantawa da karancin fitar mutane, amma Shugaban Kungiyar Kwadago a jihar Kwamred Sanusi Alhassan Maigatari na cewa,”kasancewa, yau muka fara sai mukayi tattaki daga Jami’ar tarayya ta Dutse zuwa harabar sakatariyar kungiyarmu, inda mukayi lacca kan muhimmancin wannan zanga zanga kuma a gobe rana ta biyu zamu yi tattaki zuwa gidan gwamnati domin mika sako ga gwamna”.

A jihar Zamfara ma ranar farko ta zanga zangar ‘yan kwadagon ta fuskanci rashin fitar Jama’a, sai dai sakataren NLC a jihar Kwamred Ahmad Gusau yayi tsokaci, ya na mai cewa Ita kalma ta kwadago, ai dan kabo-kabo dan kwadago ne, mai keke NAPEP dan kwadago ne, hatta mai toya kosai a bakin titi ‘yar kwadago ce, don haka duk wadanda suka zo taron zanga zangar ai ‘yan kwadago ne”.

Kodayake ‘yan kwadagon sun mika rubutacciyar takarda ga mataimakin gwamnan jihar Sanata Abubakar Umar, amma rahotanni sun ce babu wani armashi dangane da yadda al’amuran suka wakana a can.

Sai dai a jihar Sokoto bayan tattakin da ‘yan kwadagon su kayi, Shugaban Kungiyar NLC a jihar Kwamred Abdullahi Aliyu ya ce, “gaskiya mun yi farin ciki ga kwamarawa ‘yan gwagwarmaya da kuka fito kuka yi biyayya ga umarnin kungiya ta kasa, wannan zanga zanga ta kunshi komai, da tsadar rayuwa da rashin tsaro da sauran matsaloli da suke damun dan Najeriya”.

A iya cewa, ranar farko ta wannan zanga zanga ba samu ta gomashin da ake zato ba, a shiyyar arewa maso yamma, musamman la’akari da yadda mutane suka ci gaba da zirga zirga a titunan biranen Kano da Katsina da Sokoto da sauran garuruwa duk da cewa, suna korafi game da tsadar ruwa.

A saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Ta NLC Ba Ta Yi Armashi Ba A Arewa Maso Yammacin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG