Tarayyar Afirka tace zata kafa wani kwamiti shugabannin kasashe da nufin warware rikicin siyasar Ivory Coast.
Shugaban Mauritania Mohammed Ould Abdel Aziz, ya fada jiya jumma’a cewa, kwamitin zai fidda rahotonsa cikin wata daya,kuma zai zama wajibi a mutunta sakamako da ya bayar a hukumance.
Da yake magana gabannin taron kolin kungiyar a Addis Ababa, babban birnin Habasha,shugaban na Mauritania yace kwamitin zai kunshi shugabannin kasashe biyar,kuma shine zai jagoranci kwamitin, kuma za’a zabi sauran wakilan kwamitin cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Mauritania ce take rike da shugabancin majalisar tsaro da zaman lafiya na kungiyar. Tunda farko a jiya jumma’a mai shiga tsakani na kungiyar,wanda har wayau shine PM Kenya Ra’ila Odinga, ya yi kira da a yi shawarwari kai tsaye tsakanin mutanen biyu dake ikirarin shugabancin Cote’ D’voire.