Wannan aiki da shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da shi a ranar Juma’a, zai maida hankali ne a kan daruruwan iyalai a wasu manyan birane, ciki har da Chicago da Los Angeles da kuma New York.
Mutane na shigo mana cikin kasa ta barauniyar hanya, mu kuma zamu bi doka mu mayar dasu kasashen su, inji Trump.
Ma’aikatan na kwastam zasu auna bakin haure galibi masu hadari ga jama’a. Darekta mai rikon kwarya a hukumar shige da fice ta Amurka Mathew Albence ya ce an gano bakin hauren ne a cikin takardun kotuna masu shari’a a kan bakin haure.
Wannan aikin kai samame a kan bakin haure da gwamnatin Trump ta fara, ana sa ran zai farantawa wadanda suka zabe shi rai, saboda ya ciki musu alkawarin da ya dade yana fadin zai sa kafar wando daya da bakin haure marasa izinin zama kasar. Jam’iyar adawa a nan Amurka ta Democrats tayi Allah wadai da wannan aiki da ta kira rashin Imani da kuma auna iyalai da galibi sun fito ne daga kasashen tsakiyar nahiyar kudancin Amurka da suka zo ci rani.
Facebook Forum