Wannan aikin kamen da shugaba Donald Trump ya tabbatar da shi a ranar juma’a, zai auna daruruwan iyalai a birane da dama ciki har da Chicago da Los Angeles da kuma New York.
Jami’an hukumar kwastam zasu fi auna galibi mutane da suka fito daga kasashen tsakiyar nahiyar kudancin Amurka ne wadanda ake musu shari’a a kotunan bakin haure, inji darekta mai rikon kwarya a hukumar Mathew Albence.
Ana sa ran sanarwar da shugaban kasar dan Republican ya bayar a wurin wani taron gangamin siyasa game da daukar matakai a kan bakin haure, ‘yan kasa da suka zabe shi zasu yi na’am da sanarwar. Su kuwa ‘yan Democrats sun yi Allah wadai da wannan aikin kamen, aikin da suka bayyana shi na rashin imani dake auna iyalai.
Akasarin shugabannin hukumomin birane da dama, yawanci ‘yan Democrats sun yiwa dokokin biranen su gyaran huska ta yanda ba zasu amince da wannan aiki da hukumar kwastam ta fara ba na mayar da mutane zuwa kasashen su.
Facebook Forum