Jakadan Birtaniya a Amurka Kim Darroch ya sanar da murabus dinsa a yau Laraba, yana mai cewa "ba zai iya ci gaba da aikinsa ba" biyo bayan kwarmata bayanan diplomasiyya, wadanda ke dauke da batanci ga shugaban Amurka Donald Trump.
"Ko da yake aikina ba zai kare ba har sai zuwa karshen wannan shekarar, na yi imani da halin da ake ciki a yanzu, abin da ya fi dacewa shi ne a sake zaben sabon jakada," Darroch ya ce a cikin wata sanarwa.
Darroch Ya kasance babban jami'in diflomasiyyar Birtaniya a Washington tun shekarar 2016.
Ya kwatanta Trump din a matsayin “dan koyo," "matsoraci," kuma "marar kwarewa," sannan gwamnatinsa kuma "rikitacciyar ce da babu kamarta."
Facebook Forum