Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Tsohon Dan Wasan Kano Pillars Musa Kofar Mata


Bello Musa Kofarmata
Bello Musa Kofarmata

Dan wadan kwallon kafa Kofarmata da yayi wasa a wasu kasashe waje ya rasu da yammacin jiya Talata a garinsa Kano bayan ‘yar gajeruwar jinya, yana da shekaru 34 da haihuwa.

A yau Laraba ne aka yi jana’izar maragayin kuma aka binne shi a gidan iyalansa a Kofarmata dake jihar Kano bisa tsarin addinin Musulunci.

Kofarmata ya fara kwallonsa ne a shekarar 2007 tare da kungiyar Buffalo F.C ta Kano. A cikin wannan shekarar ce kuma ya koma kungiyar Kano Pillars. A shekarar 2010, ya koma da wasansa zuwa Heartland FC ta Owerri kana ya sake komawa Kano Pillars a shekarar 2012, kafin daga bisani ya koma Elkanemi Warriors ta Maiduguri.

Marigayin ya kammala yarjejeniya da kungiyar IK Start ta kasar Norway, bayan wasannin jarrabawa da ya yi da kungiyar. A lokacin da yake tare da Kano Pillars, ya yi nasara lashe kambin Premier League taNajeriya a shekarar 2007 da 2008 kana shine zakara mafi zura kwallo da kwallaye 11.

A cikin watan Agustan shekarar 2008, Kofarmata ya yi jarrabawa da clob din LASK ta kasar Austria har ya yi mata wasan zumunci guda daya. Dan wasan gaban ya baro Turai ya koma Kano Pillas a farkon kakar shekarar 2008. Ya shiga kungiyar Heartland a Janairun 2010 a kan kudin Naira miliyan 10. Bayan shekara daya da rabi, ya bar Heartland ya kuma sanya hannu a kan kwantaragi da Kano Pillars.

Marigayi Kofarmata, yana cikin tawagar ‘yan wasan Najeriya a gasar FIFA ta cin kopin zakarun kasar da shekaru 20 a kasar Canada. Ya yi wasansa na farko da Super Eagles ne a watan Maris din shekarar 2010 a wasan da Najeriya ta lallasa DR Congo da ci 5-2 a birnin Abuja, kuma ya shiga wasan ne ta hanyar musaya.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG