"Ina farin cikin bayyana muku cewa Amurka ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da ta cimma tare da Mexico, a don haka an dakatar da haraji da Amurka ta shirya aiwatar da shi a kan kayayyakin Mexico da zai fara aiki a yau Litinin, har sai baba tagani", inji shugaba Trump a wani sakonsa na twitter.
A nata bangare, Mexico ta amince da daukar kwararan matakai na dakile kwararan bakin haure da suke ratsawa da ta iyakar kudancinta. Ana daukar wadannan matakai ne domin rage kwararan bakin haure ko kuma hana bakin haure da basu da izini daga Mexico zuwa Amurka a cewar Trump.
Tun da safiyar jiya Juma’a, Trump ya fada cewa akwai alamar nasara da zata kai bangarorin biyu ga cimma yarjejeniya a kan dakatar da batun haraji saboda hana bakin haure shiga iyakar Amurka. Koda yake ya kara da cewa, idan basu cimma yarjejeniyar ba, toh Mexico zata rika biyan harajin kashi biyar cikin dari daga yau Litinin.
Jami’an Amurka da na Mexico sun koma kan teburin tattaunawa ne a jiya Juma’a a karo na uku domin nemo baki zaren dakile kwararn bakin haure daga nahiyar tsakiyar Amurka dake ketara iyakar kudancin Amurka, lamarin dake barazana ga kasuwanci tsakanin kasashen makwabta.
Facebook Forum