A yau Juma’a ne Jami’ai daga Amurka da Mexico suke komawa kan teburin tattaunawa, don neman hanyar da za’a magance matsalar kwararowar baki haure daga kasashen nahiyar Amurka ta tsakiya, zuwa kan iyakar kudancin Amurka da ya janyo barazanar cinikayya tsakanin kasashen makobtan juna.
A jiya Alhamis Amurka ta matsawa Mexico don ta kara kokarin hana karuwar bakin haure daga nahiyar Amurka, da suke tunkaro arewaci don zuwa Amurka.
Yayin da shugaba Donald Trump, ya sake sabunta barazanar sa ta saka harajin kashi biyar cikin dari akan dukkan kayayyakin dake shigowa daga Mexico a sati mai zuwa idan dai ba’a cimma wata yarjejeniya ba.
Mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence, yace ana samun ci gaba a zantawar da suke da Mexico a wannan satin.
Sai dai amma ya kuma ce Amurka tana so kasar Mexico ta kara kokari, don hana kwararowar dubban bakin haure dake fitowa daga kasashen Guatemala, Honduras, da kuma El Salvador.
Facebook Forum