Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Bakin Haure Sama Da Mutane 50 Yan Afrika Suna Kokarin Shiga Jihar Texas


A family from Haiti approaches a tent in Saint-Bernard-de-Lacolle, Quebec, stationed by Royal Canadian Mounted Police, as they haul their luggage down Roxham Road in Champlain, N.Y., Aug. 7, 2017.
A family from Haiti approaches a tent in Saint-Bernard-de-Lacolle, Quebec, stationed by Royal Canadian Mounted Police, as they haul their luggage down Roxham Road in Champlain, N.Y., Aug. 7, 2017.

Jami’an tsaron kan iyaka sun kama sama da bakin haure ‘yan Afrika dari da hamsin suna kokarin shiga jihar Texas ta kan iyakar kudancin kasar, makon da ya gabata, bisa ga cewar hukumar kwastan da kare kan iyakoki.

Ranar asabar jami’an suka kama wani gungun bakin haure 37 daga Afrika ta tsakiya wadanda suka tsallako suka shiga Amurka,hukumar tace bakin hauren sun hada da kananan yara daga Damokaradiyar Jamhuriyar Congo.

Ranar alhamis da ta gabata da yamma jami’an tsaron kan iyaka suka kama wani gungun ‘yan Afrika su 116 suna ketare teku a yankin Del Rio.

An nuna bakin hauren a wani hoton bidiyo sun dora ‘ya’yansu da ‘yan komotsansu a ka, suna ketawa cikin ruwa. Rahotannin sun nuna cewa mutanen sun fito ne daga kasashen Angola, Kamaru da kuma Congo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG