Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ba Sojojin Nijer Gudummuwar Jirgin Sama Don Yaki Da ‘Yan Ta’adda


Amurka Ta Baiwa Nijar Jiran Sama Na Yaki
Amurka Ta Baiwa Nijar Jiran Sama Na Yaki

Gwamantin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijer gudummuwar jirgin sama samfarin Hercules C 130 domin amfanin sojojin kasar a yakin da suke kafsawa da 'yan ta'adda.

A yayin wani biki da aka shirya a filin jirgin saman sojan da ake kira Escadrille a Yamai, tawagar jami’an diflomasiyya da hafsoshin sojan Amurka ta damka wa makullan wannan jirgi samfarin Hercules C 130 a hannun ministan tsaron Nijer Alkassoum Indatou da ke samun danne gargadar manyan hafsoshin sojan wannan kasa.

Jirgin wanda ke share km 537 a duk awa tallafi ne daga gwamatin Amurka domin amfanin askarawan Nijer a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda kuma a cewar Manjo Jarar James Kriesiel na rundunar sojan National Guard muhimmancin Nijer a yau a idon duniya ya kai matsayin da za ta sami kulawa ta musamman.

Da yake karbar wannan tallafi Ministan tsaron kasa Alkassoum Indatou ya ce mallakawa Nijer wannan katafaren jirgin soja babban ci gaba ne a kokarin da kasar ta sa gaba wajen neman kayan aiki a wannan lokaci na matsalar tsaro.

"Nijar kasa ce mai fadin gaske kuma yawan sojojinta takaitacce ne, lokuta da yawa mu kan kwashe dakarunmu daga fagen daga zuwa wani fagen faman na daban, kuma jirgin nan da ku ka mallaka mana ya sha taimaka wa wajen gudanar da aiki," cewar Indatou.

Babban kwamandan rundunar mayakan saman Nijer Kanar Mainassara da ke farin cikin samun wannan kayan aiki, shi ma ya yaba da gudummuwar ya kuma bayyana irin yadda sojojin Nijar suka ci moriyar jirgin kafin Amurka ta mallaka ma su shi a yau Laraba 8 ga watan Disamba don ci gaba da aikin dindindin.

Jirgin wanda a yanzu haka ke filin jirgin sojan sama na runduna ta 101 wato Escadrille da ke birnin Yamai, shine jirgi na 2 da kasar Amurka ke ba Nijer a cikin wannan shekara ta 2021 yayin da aka bayyana cewa nan gaba a watan Afrilun 2022 za a kuma sake ba Nijer din wani jirgin sojan banda wadanda ke ayyukan sintiri a yanzu haka a sararin samaniyar Nijer da makwaftanta abinda ya kara fayyace kyakyawar niyyar Amurka wajen ganin an murkushe ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

Amurka Ta Ba Sojojin Nijar Gudummuwar Jirgin Sama Don Yaki Da ‘Yan Ta’adda
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG