Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Da Hukumomi a Najeriya Na Ci Gaba Da Kwato Wa Yara Hakkokinsu


yara
yara

A Najeriya kungiyoyi da hukumomi da ke fafatukar kare hakkokin bil'adama na ci gaba da daura damarar ceto rayukan jama'a musamman kananan yara da kan iya fadawa tarkon cin zarafi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da kungiyoyin kare hakkokin bil'adama suka sha alwashin ci gaba da zakulo wadanda aka ci zarafin su domin daukar matakin da ya dace, kamar batun wani yaro mai suna Jibril Aliyu wanda a watan Agustan shekarar 2020 mahaifinsa ya daure sa cikin dabbobi tsawon lokaci a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya. Tun daga wannan lokacin gwamnati ta karbi ragamar kula da yaron a karkashin kulawar Dr. Aminu Haliru Bunza na asibitin Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi.​

Duba da halin kunci da yaron ya shiga a baya, yanzu bayan mayar da shi ga danginsa gwamnatin ta ce ta dauki matakai na kula da walwala, abinci da lafiyarsa, a cewar mashawarciyar gwamna a fannin kula da mata da kananan yara Zara'u Wali.

Fafutukar da hukumomi da kungiyoyin kare hakkokin bil'adama ke yi a Najeriya, ana iya cewa ta na yin alfanu a wani bangaren musamman duba da yadda gwamnatoci ke samar da dokokin kare hakkokin bil'adama da kuma ceto rayukan wadanda suka fada tarkon cin zarafi.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin cewa akwai bukatar gwamnatoci da ma al'umma baki daya kowa ya kula da nauyin da ya rataya akan sa, tare da bayar da hakkoki ga masu su, abinda kan iya sa a kaucewa matsalolin cin zarafi da kyautatuwar lamurra a Najeriya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Kungiyoyi Da Hukumomi a Najeriya Na Ci Gaba Da Kwato Wa Yara Hakkokinsu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00



XS
SM
MD
LG