Yayin da sojojin ruwa na Amurka su ka danna zuwa yankin ruwayen Koriya a matsayin gargadi ga Koriya Ta Arewa, McMaster ya gaya ma kafar labarai ta FOX Newa cewa, "Gwamnati ce marar natsuwa, wadda a yanzu kuma ta zama mai iya yin makaman nukiliya ... Saboda haka Shugaban kasa ya gaya ma na cewa mu kasance a shirye saboda za mu gabatar masa da jerin zabi na kawar da wannan barazanar da mutanen Amurka da abokanmu da kuma da kuma masu alaka da mu a yakin."
McMaster ya bayyana shawarar da Amurka ta yanke ta tura bataliyar Carl Vinson don ta kare muradun Amurka a yankin na Yammacin Pacific da "abin da ya dace." Ya ce Trump da Shugaban China Xi Jinping sun amince a ganawarsu ta makon jiya a Florida cewa takalar da Koriya Ta Arewa ta ke yi ta wajen kirkiro makamin nuliliya ba za a lamunta da shi ita ba.
"Shugabannin da su ka gabata da kuma Shugaba Trump duk sun amince cewa abu ne da ba za a lamunta da shi ba, don haka abin da ya kasance wajibi shi ne a kawar da nukiliya daga wannan yankin ruwayen," a cewar McMaster.
Koriya Ta Arewa dai ta yi ta kokarin kirkiro makamin nukiliya wanda zai iya isa Amurka, wato tazarar kilomita 8,000. Ya zuwa yanzu dai ta kaddamar da gwaje-gwajen nukiliya har biyar kuma mai yiwuwa ta na kan shirin na shida.
Facebook Forum