Dakarun sojin ruwan Amurka zasu tura kungiyoyin mayaka bangaren tsibirin Koriya domin kara kwarjinin kasancewar Amurka a yankin da kuma tura sako ga Koriya ta Arewa, wacce a satin da ya gabata ta gudanar da gwajin makami mai linzami sanfurin Ballistic duk da majalisar warware matsalolin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta haramta ire iren wadannan gwaje gwaje.
Kungiyar dakarun Carl Vinson Strike Group na cikin shirye shiryen zuwa gabar tekun Singapore ne inda aka shirya zasu tafi zuwa Austarlia lokacin da Kwamandan Dakarun Amurka dake a yankin Pacific ya basu umarnin a juya ragamar jirgin zuwa Arewa.
Kwamandan Dakarun Amurka na yankin Pacific ya fadawa muryar Amurka cewa “Har ya zuwa yanzu Koriya ta Arewa itace Barazana ta farko a yankin sakamakon ganganci da kuma kin daina gwajin makami mai linzami wanda zai bada damar cigaba da gwajin makamin Nukiliya.”
Pyongyang ta cigaba da yin biris da gargadin kasashen duniya akan daina gwajin makamai masu linzami da kuma na’urar nukiliya.
Facebook Forum