Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin Kasashen Duniya Kan Harin Da Amurka Ta Kai Syria


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Kawayen Amurka da dama sun bayyana goyon bayansu akan matakin da Amurka ta dauka akan Syria, yayin da Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin na yi wa harin kallon “Mummunan mataki kan wata ‘yan tacciyar kasa mai cin gashin kanta” kuma akan “dalili mara tushe.”

Masu sa ido a Syria sun ce harin da aka kai kan filin jirgin ya kashe kimanin sojojin Syria hudu, yayin da Jami’an Syria suka ce mutane shida ne suka mutu wasu da yawa kuma suka jikkata.

Wata cibiya mai nazarin al'amura a Syria ta ce harin na Amurka ya janyo mutuwar akalla sojojin Syria hudu.

Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin wanda babban aminin Shugaban kasar Syria Bashar al Assad ne, ya ce bai yarda Syria na da makamai masu guba ba.

Wannan mataki ya sa Rasha ta ce ta dakatar da yarjejeniyar fahimtar juna da suka kulla da Amurka kan matakan tabbatar da tsaron lafiyar jiragensu dake shawagi a sararin samaniyar Syria.

Ita ma dai kasar Iran ta yi Allah wadai da wannan hari inda ta ce “matakin da Amurka ta dauka akan kanta na da hadari kuma ya ruguza ginshikin dokokin kasa da kasa.”

Sai dai a daya bangaren kuma mataimakin Firai ministan kasar Turkiya Numan Kurtulmus ya yaba da harin na Amurka.

A lokacin wata hira da wani gidan Talabijin, Kurtulmus ya ce harin da Amurka ta kai akan filin jirgin sama na Syria ya yi kyau kuma lokaci ya yi da za’a dakatar da ta’addancin gwamnatin.”

Sauran kasashen da suka goyi bayan harin da Amurka ta kai sun hada da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.

Yadda Amurka Ta Kai Harin

Da safiyar yau juma’a ne dakarun Amurka suka harba makamai masu linzamin cikin Syria.

Makaman masu linzami wadanda ake wa lakabi da Tomahawk guda 59 aka cilla da misalin karfe 4:40 na asubahin kasar Syria daga kan wasu jiragen ruwan yakin Amurka guda biyu da aka girke a tekun Meditareniya.

An dauki akalla mintoci uku zuwa hudu ana harba wadannan makamai, a cewar jami’an Amurka.

Rahotanni sun ce dakarun Amurka sun kai harin ne kan filin jiragen sama na Shayrat dake Yammacin Syria.

Amurkan ta dauki wannan mataki ne sakamakon harin makami mai guba da ake zargin dakarun Syria sun kai kan fararen hula wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100 ciki har da kananan yara a yankin Idlib.

Mabanbantan Ra'ayi a Majalisar Dokokin Amurka

Harin da Amurka ta kai Syria ya samu yabo tare da fuskantar suka daga bangarorin dake majalisar.

Yayin da 'yan Republican ke nuna goyon bayansu kan wannan mataki, 'yan jam'iyar Democrat Allah wadai suka yi da harin.

"Ina ganin wannan harin da Amurka ta kai, zai aike da sako ga kawayenmu na Sunni a kasashen larabawa da cewa Amurka ta farfado kuma wannan gargadi ne ga kasashen Korea ta arewa da Iran da Rasha cewa Amurka na da niyyar sake zama jagora." In ji Shugaban masu rinjaye a majalisar Mitch McConnell.

Sai dai ba ta wannan fuskar 'yan Democrat suke kallon wannan hari ba, domin ana su ganin bai dace shugaba Trump ya tsallake majalisar ya yi gashin kansa ba.

"Idan shugaban ya na so ya dauki matakin soji a Syria, ya zama dole ya zo gaban majalisa ya nemi izni." Shugabar marasa rinyaje Nancy Pelosi ta ce.

Masu lura da al'amura da dama na ganin wannan wani sabon babi ne aka bude a rikicin na Syria wanda ke bukatar a bi shi a hankali, lura da yadda ya ke kara samun bangarori biyu - da masu goyon bayan Syria da masu mara wa Amurka baya.

Hakan ne ma ya sa a daidai lokacin hada wannan rahoto, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da wani taro domin yin dubi kan harin da Amurka ta kai Syria, taron da Rasha ta nemi a yi cikin gaggawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG