Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Batun Yaki Da Boko Haram


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, a ziyarar da ta kai kasar Kamaru
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, a ziyarar da ta kai kasar Kamaru

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, ta ce Amurka na goyon bayan kasar Chadi da ke gabashin Afirka da makwabtanta a kan batun yaki da Boko Haram.

Power na kan ziyartar kasashe uku na yankin na gabashin Afirka ne, don jaddada goyon bayan Amurka game da yaki da 'yan bindigar, wadanda su ka fi karfi a yankin Tafkin Chadi, inda kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru ke iyaka da juna.

Power ta fadi jiya Laraba a N'Djamena babban birnin kasar Chadi cewa Amurka na cigaba da goyon bayan yakin da ake da Boko Haram ta wajen samar da kwararru da bayanai da horo da kayan aiki da kuma makamai ga gamayyar sojojin yankin, wadda aka kafa don tsai da hare-hare da yinkurin kungirar na kama karin yankuna.

Ta sake jaddada abin da ta fadi ranar da ta gabata a kasar Kamru, cewa yaki da Boko Haram ya wuce batun amfani da karfin soji. Ta ce dole yakin ya hada da aiki da gaskiya a fannin siyasa, da kare 'yancin dan'adam, da kuma mutunta doka da oda.

Da aka tambaye ta kan makomar wadanda kama su da 'yan Boko Haram su ka yi ya fi jawo ca, wato 'yan matan Chibok da aka sace daga wata makaranta kimanin shekaru 2 da su ka gabata, Power ta yi nuni da cewa 'yan mata sama da 200 din wani bangare ne kawai na dubban mutanen da 'yan Boko Haram su ka cutar. Ta ce sam tsawon lokace ba zai sa kudurin ganin an sake hada yaran da iyalinsu ya dusashe ba.

XS
SM
MD
LG