Kungiyar likitocin sa-kai ta doctors without borders sun fadi cewa ba za'a iya cimma kudurin kawar da cutar sida a doron duniya a shekarar 2020 ba sai dai in ma’aikatan jinkai sun gane cewa akwai bukatar karin aiki tukuru a yankin Afrika ta yamma da ta tsakiya, inda adadin masu cutar ya ragu in aka danganta da yankin kasashen da ke kudu da hamada.
Likitocin sa-kan sun fidda wan irahoto yau Laraba mai cewa, maida hankalin kan kasashen Afrika da cutar sida ta fi Kamari da aka yi ya sa ba a iya maida hankali akan bukatun yankunan Afrika ta yamma da ta tsakiya ba.
Rahoton ya ce yayinda yaduwar cutar sida ta ragu a wannan yankin, inda kashi 2.3 na al’ummar yankin ke dauke da kwayar cutar, duk da haka wannan adadin ya rubanya har sau 3 a duniya, haka kuma wasu sassan wannan yankin na da kashi kusan 5 na yaduwar wannan cutar.
Rahoton kuma ya bukaci cibiyoyin MDD, da cibiyoyin dake bada gudumuwa daga kasashn Turai, da gwamnatoci da kuma kungiyoyin al’umma da su fito da wani shiri wanda zai zaburar da jinyar cutar a kasashen Afrika ta yamma da ta tsakiya inda kasa da kashi daya cikin 3 din al’umma dake da bukatar magunguna kawai ke samun jinya yanzu haka.