Kin zuwa Juba babban birnin Sudan ta kudu da shugaban ‘yan tawaye Riek Machar yayi yau Talata, karo na biyu ke nan cikin wannan makon, ka iya warware yajejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a kasar da yaki ya daidaita.
An sa ran Mr. Machar zai koma babban birnin kasar cikin makon nan don a kafa gwamnatin hadin guiwa da shi tare da shugaba Salva Kiir bayan shekaru 2 da rabi da aka kwashe ana yaki a kasar, amma amma gab da wannan hidimar Machar ya soke tafiyarsa zuwa babban birnin.
Fetus Mogae, shine shugaban kungiyar kasash da ke sa ido akn yan=rjejeniyar zaman lafiyar, ya kira taron gaggwa gobe Alhamis in Allah ya kaimu a Juba tsakanin gwamnati da jami’an ‘yan tawayen du zummar shawo kan lamarin.
Jakadan Amurka Mr. David Pressman, ya fada jiya Talata a lokacin da ya fito daga wan izama na kwamitin sulhun Majalira Dinkin Duniya cewa, Amurka ba ta ji dadin kasa cika alkawarin da Machar yayi ba na komawa Juba.