Hukumomi a jihar Texas sun fara tuhumar wani matashi dan shekaru 17 da laifin kisan mutane 10, mafi aksarinsu dalibai, a makarantar Sakandare da ke Sante Fe.
Daliban makarantar sun ce, jami’an tsaro sun bayyana sunan dan bindigar a matsayin Dimitrios Pagourtzis, wanda shi ake zargi da bude wuta a makarantar ta Santa Fe da misali karfe takwas na safiyar jiya Juma’a.
Gwamanan jihar ta Texas, Greg Abbot, ya ce ‘yan sanda sun tsinci ababan fashewa, da irin kwalbar nan da ake dura mata mai ta fashe ta baza wuta idan an hurga ta, a gidan dan bindigar da kuma wata mota da aka ajiye a kusa da makarantar da aka kai harin.
Gwamna Abbot ya kara da cewa, maharin, wanda yanzu haka yana hannu ana tuhumarsa da laifukan kisa, ya so ya kashe kansa bayan da ya kai harin.
Amma bayan da aka kama shi, ya fadawa ‘yan sandan cewa ya kasa samun zuciyar daukan ran nasa.
Gwamnan jihar ta Texas ya kuma ce, an yi amfani ne da bindigogi biyu wajen kai wannan hari, wato da babbar bindiga irin ta mafarauta da kuma karama.
Ya kara da cewa duka bindigogin na mahaifin matashin ne, amma kuma babu wasu bayanai da ke nuna cewa mahaifin yana sane dansa ya dauki bindigogin, yana mai kwatanta wannan hari a matsayin “mafi muni” a tarihin harbe-harbe a makarantun jihar Texas.
Wannan hari na makarantar ta Santa Fe, na zuwa ne kusan watanni uku da harin da aka kai a makarantar Marjory Douglas High School da ke Parkland a jihar Florida, inda wani dan bindiga ya kashe dalibai 16 da malami daya.
Facebook Forum