Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Zanga zangar Kwanaki 40 Domin Yaki Da Talauci a Amurka


Wadanda suka yi fafutika da Rev Martin Luther King shekaru 50 da suka gabata
Wadanda suka yi fafutika da Rev Martin Luther King shekaru 50 da suka gabata

Marasa galihu da masu karamin albashi da shugabannin addin a duk fadin Amurka sun farfado da gwagwarmayar da Rev Martin Luther King Jr. ya kafa shekaru 50 da suka gabata kuma zasu fara zanga zanga a manyan birane da kwanaki 40

Dubban marasa galihu da masu daukan karamin albashi da masu fafatuka tare da shugabannin addinai a duk fadin Amurka, sun farfado da wata fafutuka ta marasa galihu, wacce gwagwarmaya ce ta fararen hula da Rev. Martin Luther King Jr. ya faro tun shekaru 50 da suka gabata.

A wannan shekara, za a kwashe kwanaki 40 ana zanga zanga, a sama da manyan biranen jihohin Amurka 30 da kuma babban birnin kasar na Washington.

Manufar farfado da wannan gwagwarmaya ita ce a yaki talauci da kuma banbancin samu da suka samo asali shekaru 50 da suka gabata.

A shekarar alif-dari-tara-da-sittin-da takwas, Martin Luther King, ya kafa wannan fafutuka wacce ta tattaro jama’a masu al’adu da addinai daban-daban, bayan da ya ganewa idonsa yadda ake fama da yunwa a garin Marks da ke Mississippi, kusan kilomita 113 a kudancin birnin Memphis na jihar Tennesse.

A lokacin ne ya shirya wani tattaki na marasa galihu da aka yi a nan Washington, inda suka mika bukatar neman a kyautata rayuwar jama’a da kuma karin albashi.

Masu shirya gangamin na yanzu, suka ce har yanzu ba'a cimma muradun abunda yasa Rev. King ya kafa wannan hadakar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG