Shugaban Amurka Donald Trump yace yana duba hanyar ganin kanfanin fasahan nan na kasar China ya koma bakin aikin sa cikin dan kankanin lokaci, bayan da dokokin kasuwancin Amurka suka durkusad da kanfanin
Dama Amurka ta yanke fitar da kayayyakin da kanfanin ZTE ke samarwa da wurin kashi 25 wanda kanfanin zaiyi anfani dashi wajen samar da wayoyin hannu, da sauran ayyukan da ya shafe shi.
Amurka ta dauki wannan matakin ne akan kanfanin na ZTE bayan an kama kiri-kiri tana anfani da fasahar Amurka wajen garwayawa da nata tana sayarwa kashen da Amuyrka tasa takunkumin kasuwanci , kasahen ko sun hada da Iran da Korea ta Arewa, inji wani masani harkokin fasaha.
Maaikatar cinikayya ta yanke damar da kanfanin na ZTE take dashi ne ga fasahar Amurka har sai zuwa shekarar 2025, wanda wannan ya tilasta kanfanin rufe masanaantar ta dake Shenzhen
Facebook Forum