Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Kawayenta Sun Zafafa Kai Farmaki Kan Cibiyoyin Gwamnatin Libya


Wani jirgin yaki kirar F-16 na kasar Denmark, yana tashi daga sansanin mayakan saman NATO dake Sigonella a Italiya, lahadi 20 Maris 2011
Wani jirgin yaki kirar F-16 na kasar Denmark, yana tashi daga sansanin mayakan saman NATO dake Sigonella a Italiya, lahadi 20 Maris 2011

Yayin da Rasha, da Kungiyar Kasashen Larabawa da kuma Tarayyar Kasashen Afirka suka nemi da a kawo karshen wannan farmaki kan Libya

Amurka da kawayenta sun zafafa hare-haren da suke kaiwa ta sama a kan sojojin gwamnatin Libya, suka ja burki ma farmakin da suka kai kan tungar ‘yan tawaye a Benghazi, yayin da shugaba Muammar Gaddafi ya lashi takobin fatattakar kasashen da ya bayyana a zaman na Kiristoci masu gaba da shi.

Jiya lahadi, jiragen saman yaki na Amurka, sun kai hare-hare a kan sojojin kasa na Libya da cibiyoyin tsaron samaniyar kasar, a bayan ruwan makamai masu linzami samfurin Tomahawk da aka kai kan Libya daga jiragen ruwan yaki.

Vice Admiral William Gortney na rundunar sojojin ruwan Amurka yace an lalata kusan dukkan cibiyoyin tsaron samaniya na Gaddafi a hare-haren da aka kai. Jiya lahadi da maraice an ji kararrakin fashe-fashe a Tripoli, babban birnin kasar, an kuma jefa bam aka lalata wani gini na gudanar da sha’anin mulki ‘yan mitoci kadan daga tantin shugaba Gaddafi a gidan kwanansa. Amma jami’an Amurka sun ce ba wai an kai harin ne a kan shi kansa shugaban na Libya ba. An ji kararrakin makaman kabo jiragen sama a bayan faduwar rana a birnin na Tripoli.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar kasashen larabawa, ya soki lamirin hare-haren sojan da ake kaiwa a kan Libya, yana mai fadin cewa wannan mataki ya wuce haramcin zirga-zirgar jiragen sama da kungiyar ta nemi a kafa a kan Libya. Sakatare janar na kungiyar ta kasashen larabawa, Amr Moussa, ya fada jiya lahadi cewa kungiyarsu ta nemi a kare fararen hula ne ba wai a kai musu hare-haren bam ba.

Kasar Rasha, ta yi kira ga kasashen na waje da su kawo karshen abinda ta kira yin amfani da karfi ba bisa ka’ida ba a Libya. Rasha ta ce an kashe fararen hula 48 a wadannan hare-hare.

Ita ma kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta yi kiran da a kawo karshen wannan farmakin.

Jakadun NATO sun amince da wani shiri na yin amfani da jiragen ruwan yakin kungiyar wajen hana kai makamai zuwa Libya. Amma jami’ai sun ce Turkiyya ta hau kujerar-na-ki kan yin amfani da jiragen saman NATO wajen hana jiragen sama shawagi a samaniyar Libya.

XS
SM
MD
LG