Rundunar sojin dake biyayya ga shugaba Moammar Gadhafi na Libya na ci gaba da kai hare-hare kan wasu muhimman wurare dake kusa da Tripoli, babban birnin kasar, a dai dai lokacin da ita kuma rundunar tsaron turai ta NATO ke kokarin karbar jagorancin kai hare-haren tabbatar da aiki da kudurin dokar Majalisar Dinkin Duniya na hana jiragen saman yakin Libya zirga-zirga a kan wasu kebabbun sararin samaniyar Libya.
Mayakan dake biyayya ga shugaba Ghadafi na kai hare-harensu ne kan wuraren dake hannun mayakan ‘yan tawaye dake yankin gabashin Misrata da kuma Zintan. An kuma bada sanarwar fashewar wata babbar bindigar kakkabo jiragen saman yaki a birnin Tripoli yau laraba.
A dai dai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki, kamfanin dillancin labarai na Associated ya bada rahton cewa jiragen ruwan yakin NATO dake tsaye a gabar ruwan tekun Libya sun fara gusawa domin maida martanin farmaki ta yadda za’a kaarfafa tilasta yin aiki da kudurin dokar hana Libya aiki da jiragen saman yakinta a sararin samaniya. An kuma kammala duk wasu shirye-shiryen mikawa NATO kulawa da tabbatar dayin aiki da kudurin na MDD a kan Libya.
Ta wani bangaren kuma, Kamfanin dillancin labarum Faransa ya bada rahoton cewa sojin Gwamnatin shugaba Moammar Gadhafi sun saki ‘yan jaridar nan biyu da mai daukan hotunan dake yiwa kamfanin aiki a Libya. An bada rahoton bacewar ‘yan jaridar uku ne bayan sun aike da sakon e-mail dake cewa suna kan hanyarsu ta neman labarai dake datazarar Kilomita 35 daga birnin Tobruk a daren Juma’ar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran faran yaceya jiwo daga wajen Direban motar da tuka ‘yan jaridar na cewa sojin dake biyayya ga Ghadafi ne suka kame ‘yan jaridar.