Amurka da kawayenta sun sake kai wasu hare-haren jiragen sama kan wasu kebabbun wurare a kasar Libya kusa da Tripoli, babban birnin kasar Libya.Safiyar lahadi ce jiragen saman yakin kasashen Yammacin Turai suka yi ruwan boma-bomai a kan manyan titunan birnin Tripoli domin hana motocin yakin Gwamnatin Ghadafi da tankunan yaki yin zirga-zirga.Babban hafsan rundunar sojin Amirka Admiral Mike Mullen ran lahadi yake cewa hare-haren farko da aka kai ta sama kan Libya domin tilasta aiki da kudurin MDD na hana zirga-zirgar jiragen saman Libya sun sami nasara.
Shugaba Moammar Gadhafi na Libya ya cika baki tare da bugun kirjin cewa kasar sa zata sami nasara a kan sojin taron dangin kasashen Turai ta yamma da yanzu suke harbawa sojin Libya makamai masu linzami ta jiragen sama da ruwa.
A jawabin da yayi ta gidan Rediyo da Telbijin na Libya, shugaba Gadhafi yace babu wata hujja kwakkwara da zata sa Amurka da kasashen Turai yin shisshigi a a rikicin kasarsa. Don haka yace hare-haren jiragen saman yaki kankasar Libya tamkar aiki ne irin na ‘yan ta’adda. Shugaba Gadhafi ya kara nanata cewar yana daisassun makamai, kuma ya bada umarnin bude dukkan tumbunan makaman Libya, kuma al’ummar Libya suna dauki makamai domin karekansu, yaki hakika Libya zata sami nasara a kan mayakan kasar waje. Asabar ce jiragen saman yakin Amurka da na kasashen Turaia suka kai farmaki kan wasu kebabbun wurare a Libya domin tilasta aiki da kudurin MDD na hana jiragen saman Libya zirga-zirga. Ma’aikatar tsaron Amurka ta bada rahoton cewa anyi amfani da jiragen ruwan yakin dake dauke da jiragen saman yakin Amurka da na Birtaniya wajen harba makamai masu linzami samfurin Tomahawk sama da dari da gomasha biyu a kan Libya. Jiragen saman yakin sun sami nasarar harba rokoki kai tsaye a kan wurare sama da ashirin a Libya. Gidan Telbijin na Libya ya bada labarin cewa hare-haren na Amurka da Turai sun kashe mutane 48, sannan mutane dari da hamsin suka jikkata.