Kwamitin Sulhun MDD ya bayar da iznin hana jiragen sama shawagi a samaniyar kasar Libya, matakin da yana iya janyo arangama da sojoji masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya. Kasashe 10 sun jefa kuri’ar amincewa da wannan kudurin jiya alhamis, yayin da sauran kasashe biyar na kwamitin sulhun, watau Brazil, China da Jamus da Indiya da kuma Rasha suka kaurace. Kudurin ya baai ma wakilan MDD iznin daukar dukkan matakan da suka ga sun kamata domin kare fararen hula, ciki har da haramta shawagin dukkan jiragen sama a samaniyar Libya. Har ila yau kudrin ya bayyana damuwa sosai a kan yadda al’amura ek tabarbarewa a Libya, ya kuma yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta da kawo karshen duk wani tashin hankali a kan fararen hula. Dubban mutane sun fito kan titunan birnin Benghazi, cibiyar ‘yan tawayen Libya su na murnar wannan kudurin MDD ta hanyar harba bindigogi a sama tare da cilla kayan wuta.
Mr. Gaddafi ya ja kunnen ‘yan tawayen da su yi saranda ko kuma za a far musu. Yace dakarunsa ba zasu tausaya ma wadanda suka bijire ba, ya kuma yi watsi da wannan kuduri a zaman na wofi. Amurka ta fara shirye-shiryen tabbatar da cewa an yi aiki da haramta shawagin jiragen sama. Italiya ta bayarda tayin amfani da sansanin mayakan samanta na Sigonella dake Sivcily, yayin da kasar Canada ta ce zata aike da jiragen saman yaki guda 6 zuwa yankin. Kwamitin Sulhun MDD ya bayar da iznin hana jiragen sama shawagi a samaniyar kasar Libya, matakin da yana iya janyo arangama da sojoji masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya. Kasashe 10 sun jefa kuri’ar amincewa da wannan kudurin jiya alhamis, yayin da sauran kasashe biyar na kwamitin sulhun, watau Brazil, China da Jamus da Indiya da kuma Rasha suka kaurace.