A wani zaman farko da aka yi a watan da ya gabata, Wilders da lauyoyinsa suka nemi alkalai su yi watsi da korafe-korafen da aka gabatar a gabansu, inda suka ce karar bita-da-kullin siyasa ce, wacce aka shirya domin a kassara takararsa a zaben da za a yi a watan Maris mai zuwa.
Sai dai a hukuncin farko da ya yanke, alkalin kotu a gundumar Hague, ya yi watsi da hujjar Wilders, inda ya ce shari’ar ba za ta shafi walwalar siyasarsa ba, ko kuma jam’iyyarsa ta Freedom Party.
Wannan kara da aka shigar akan Wilders ta samo asali ne daga wasu kamalamai da ya furta a shekarar 2014 a lokacin yakin neman zabe a Hague, inda ya tambayi magoya bayansa ko suna so baki ‘yan kasar Morocco da yawa su shiga kasar ko kuma akasin hakan?
Nan take dai magoya bayansa suka ce kadan su ke bukata, shi kuma Wilders ya ce, za a shirya yadda za a aiwatar da hakan.