Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristoci A Jihar Filaton Najeriya Sun Bukaci A Daina Kashe-kashe


Taron kira a daina kashe kashe a Jihar Filato
Taron kira a daina kashe kashe a Jihar Filato

Al’ummar Kiristocin Jihar Filato sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin Jihar da ke birnin Jos domin tunawa da mummunan asarar rayuka da aka yi a cikin 'yan kwanakin nan. 

PLATEAU, NIGERIA - Harin jajibirin Kirsimeti a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, da Barkin-Ladi, wanda ya hallaka rayukan mutane fiye da 160, ya dauki hankalin duniya.

Gwamnan Jihar Filato lokacin gangamin kira a daina kashe-kashe
Gwamnan Jihar Filato lokacin gangamin kira a daina kashe-kashe

Masu tattakin, karkashin jagorancin Rabaran Dokta Stephen Baba Panya, Shugaban Cocin Evangelical Winning All (ECWA), tare da hadin gwiwar kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), sun gabatar da “bukatu 10 na neman zaman lafiya” ga gwamnan jahar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang.

Rabaran Panya ya nuna jin dadinsa kan matakan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Mutfwang suka dauka, yayin da ya jaddada bukatar kara hada kai don magance hare-haren da ake kaiwa Kiristoci a jihar Filato.

Gangamin kira a daina kashe kashe a Jihar Filato
Gangamin kira a daina kashe kashe a Jihar Filato

Rev. Panya ya yi karin haske game da tsawon shekaru 22 na tashin hankali a jihar, da har yanzu ba'a sami hanyoyin daidaitawa ba.

Rabaran Panya-Baba yace rikicin na jahar Filato ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane ba tare da an gurfanar da wadanda aka samu da laifi, a gaban kotu ba.

Pastor a jihar Filato
Pastor a jihar Filato

Rev. Panya ya yi kira da a shiga tsakani cikin gaggawa, gami da samar da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Ya amince da umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar ga hukumomin tarayya domin a taimaka wa wadanda rikicin ya shafa.

Wani Pastor a lokacin taron kira a daina kashe kashe a jihar Filato
Wani Pastor a lokacin taron kira a daina kashe kashe a jihar Filato

Jagoran tattakin ya yaba wa kokarin Gwamna Caleb Mutfwang na yin Allah wadai da hare-haren da kuma bayar da agaji ga wadanda suka tsira da rayukansu.

Ya jaddada bukatar a kawo karshen hare-hare da kashe-kashen da ake ci gaba da yi, tare da neman adalci ga al’ummar kirista, cikin gaggawa.

Taron masu kira a daina kashe kashe a jihar Filato
Taron masu kira a daina kashe kashe a jihar Filato

Rabaran Panya ya bukaci babban mai shari’a na tarayya da ministan shari’a da su ayyana duk masu dauke da makamai da ke da alhakin kashe-kashen a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance.

Ya yi kira da a inganta matakan tsaro ga ‘yan gudun hijira 15,000 a Bokkos da kuma sake gina gidaje da aka lalata wa al’ummomin.

Taron masu kira a daina kashe kashe a jihar Filato
Taron masu kira a daina kashe kashe a jihar Filato

Gwamna Caleb Mutfwang, a lokacin da yake karbar kungiyar Kiristocin, ya nuna jin dadinsa da goyon bayan da aka ba shi, ya kuma ba da tabbacin mika bukatarsu ga shugaba Tinubu cikin gaggawa.

Gwamnan ya nuna amincewarsa da kudurin da shugaban Kasa Bola Tinubu ya fara dauka na kawo karshen tashe-tashen hankula.

Ya kuma jaddada aniyar tabbatar da tsaron kasar, yana mai alkawarin cewa zubar da jini ba zai tafi a banza ba.

Gangamin kira a daina kashe kashe a Jihar Filato
Gangamin kira a daina kashe kashe a Jihar Filato

Fitattun shugabannin cocin, ciki har da shugaban CAN na jihar Filato, Rabaran Fada, Polycarp Lubo, Archbishop Katolika na Jos, Mathew Ishaya Audu, Bishop Methodist, Nkechi Nwosu, shugaban COCIN wanda Rabaran Pokol, shugaban PFN ya wakilta, Rabaran Dunka Gomwalk, OAIC- Apostle M. Ewurum, Rabaran Stephen Dangana da Rabaran Gideon Para-Mallam, sun shiga wannan tattakin na zaman lafiya, inda suka nuna hadin kai da kuma nuna damuwarsu ga halin da al’ummar yankin ke ciki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG