Rahotanni dai na nuni da cewa wani direba ne dake tuka wata karamar mota kirar starlet, ‘dauke da bam din cikin bakar leda, inda nan take ya samu wasu yara dake bakin titi suna wasa a nan ne ya yaudaresu da cewa wai sako ne aka bashi ya baiwa baban wani yaro.
Bayan da yaran suka karbi ledar da zummar zasu kai gida, tafiyar direban ke da wuya bam din ya fashe kafin su karasa gida. Nan take ya kashe yara biyu wasu kuma suka raunata, inda aka garzaya da su asibiti.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawan ta bakin kakakinta SP Othman Abubakar, ta tabbatar da faruwan lamarin.
Ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya data dau alhakin tashin bam din, to sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro ke gargadin cewa bayanai na nuni da cewa ‘yan ta’adda yanzu na sauya salo, don haka ake gargadin jama’a da akula, musamman a wuraren hada hadar jama’a da kuma wuraren ibada, kamar yadda kakakin rundunan yan sandan yayi Karin haske.
Yankin Hong dai na daga cikin yankunan da a baya suka fada hannun mayakan Boko Haram, kafin daga baya dakarun Najeriya bisa tallafin yan sakai suka kwato yankin, wanda kuma tun wancan lokaci ba’a sake jin wani abu ba sai yanzu.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum