Majalisar Dattawan Najeriya ta baiwa hukumar alhazan Najeriya umurnin ta rage kudin kujerar zuwa hajji daga Nera miliyan daya da dubu dari biyar da ta sa yanzu.
Sanata Ibrahim Kabiru Gaya daya daga cikin wadanda suka kawo kudurin rage kudin a gaban majalisar ya fada cewa tuni wasu ma da suka soma ajiye kudinsu a asusun da hukumar alhazai ta bude domin tara kudin tafiya sun fara janyewa.
A cewar Sanata Gaya kudin da aka sa yayi yawa saboda gwamnatin tarayya take daukan alhazan kuma suna biyan kudin tafiya. Yace akwai kamfanoni dake zaman kansu suna daukan masu tafiya da kansu amma suna biyan Nera miliyan daya ne da dubu dari biyu duk da cewa kamfanonin na basu gidajen kwana da abinci da mota, ga kuma babu cunkoson jama'a. Amma alhazan da hukumar alhazai zata dauka sai an yi hayaniya zuwa da dawowa ga matsalar abinci da wurin kwana. Yace hanya ce kawai ta ba wasu kwangilar kai abinci domin su cuci alhazai.
Shi ma Sanata Bukar Madawakin Daura yace ana iya samun mafita kan abubuwan da suka sa kudin kujerar ya haura fiye da miliyan daya. Yace kusan watanni uku da suka wuce shugaban hukumar alhazai ya fito yace kudin kujerar bana ba zai kai na bara ba a lokacin da dala tana wajen Nera dari biyar. Yanzu ta sauko amma kuma gashi an fito da farashi mai tsada abun da ya sa suke ganin ba'a yiwa mutane adalci ba.
Sanata Bukar da majalisar dattawa sun kira gwamnati ta duba farashin kudin jirgi da farashin wurin zama da kuma shirin raba abinci. A bar mutane su sayi abincin da zasu ci saboda wani ma azumi zai yi.
Ahalin yanzu majalisar ta ba kwamiti dinta dake kula da harkokin kasashen waje mako daya yayi bincike ya bada rahoto.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum