Yanzu yau rundunar 'yansandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane 14 tare da wasu 24 da suka jikata sakamakon kunar bakin waken da wasu 'yan kungiyar Boko Haram suka kai.
A daidai lokacin ne kuma wasu 'yan Boko Haram suka yi kokarin kai hari a Jiddar-Polo wata unguwa a birnin Maiduguri.
Kwamishanan 'yansandan jihar Mr. Daniel Chukwu ya shaidawa manema labarai cewa bam din farko ya tashe ne a kauyen Kacallari dake karamar hukumar Jeni yayinda mutane ke fitowa daga sallar magariba inda mutane shida suka mutu da kuma wasu 24 da suka samu raunuka daban daban..
Akwai kuma wani bam din na biyu da ya tashi a wuraren yankin Chad Basin wanda ya kashe mutane uku. A nan bangaren kuma bam na uku ya tashi da ya kashe mutum guda.
Kokarin da 'yan Boko Haram suka yi na kutsawa cikin birnin Maiduguri ta Jiddari-Polo ya haddasa mutuwar mutum daya wanda har yanzu ba'a tantanceshi ba.
Tun a daren jiya din ne sojoji da 'yansanda suka dakile harin, inji kwamishan 'yansandan, lamarin da ya sa wadanda suka arce daga gidajensu sun soma komawa.
Kawo yanzu an kame wani dan Boko Haram daya kana an kashe wasu guda uku sakamakon musayar wuta da suka dinga yi da jami'an tsaro.An kuma gano wasu bindigogi kiran AK47 da wasu bamabamai kiran gida.
Maharan Boko Haram din sun kone gidajen 'yan gudun hijira guda ishirin wadanda suke daf da shiga cikin garin Maiduguri.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum