Cibiyar kare al'umma ta Italiya ce ta ba da wannan adadin da daren jiya Laraba, wanda dori ne kan adadin 124 da aka bayar kafin nan a jiya din. Masu ayyukan ceto na cigaba da kwakulo baraguzai don nemar wadanda abin ya rutsa da su.
Tun da farko a jiya Larabar, Firaminista Matteo Renzi ya yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen tafiya wuraren da abin ya faru, inda ya gaida masu ayyukan ceton. Renzi ya kuma tattauna da Ministan Ayyuka da kuma shugaban cibiyar Kare Al'ummar.
Amma ya ki ya bayyana ma manema labarai komai, ya ce yanzu ba lokacin magana ba ne. Tunda farko, Renzi ya ce, "Babu wani iyali ko birni ko garin da za a ki kula shi."
Hukumar nazarin karkashin kasa ta Amurka ta ce karfin girgizar kasar ya kai 6.2 a ma'auni, kuma tushen girgizar kasar na wani wuri mai nisan kilomita 10 kudu maso gabashin garin Norcia.