Wani daga cikin ‘yan kasuwar ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Sule Mummuni Barma cewa dan kasuwar da ke samun jikka uku ko biyu na Sefa irin kudin kasar a da, da wuya ya iya samun jika dari a wannan yanayi da kasar take ciki, ya kara da cewa wwasu lokutan da dama sai dai dan kasuwa ya bude shago har ya kulle bai sami ko sisi ba.
Halin talauci da ‘yan kasar suka shiga a baya bayan nan wani abu ne da ya dauki hankalin masana a fannin tattalin arziki wadanda ke yiwa lamarin fassara irin wadda ta jibanci harkokin hada hadar shigi da fici na kudi daga aljihun gwamnati zuwa na jama’ar kasa kamar yadda Dr Soli Abdullahi masani a harkokin tattalin arziki ya bayyana.
Sai dai kuma masu ra’ayin gwamnatin kasar kamar su Alhaji Usmana na ganin cewa wannan matsala ce data gama duniya, kuma ya kara da cewa idan aka kwatanta lamarin da wasu kasashe makwabta misali irin su Najeriya, Nijer sai sambarka.
Wani dalili da masana suke dauka a matsayin hujjar dake zama musabbabin dabaibayewar tafiyar tattalin arzikin Nijer a shekarun baya bayan nan shine yadda mutane ke wawashe kudaden gwamnati domin azurta kawunan su.
Kakain jam’iyyar PNDS mai mulki ya ce batun ba haka yake ba domin kuwa gwamnatin kasar na gudanar da ayyuka kamar yadda ya kamata dan haka maganar rub da ciki kan dukiyar kasa duk maganar kawai ce.
Domin Karin bayani saurari rahoton Sule Mummuni Barma.