Malam Kasimu Ummar Sokoto na daya daga cikin jerin manyan malaman da suka ja ragamar masu zanga zanagar kuma ya bayyana cewa sun fito ne domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsare shugaban nasu da gwamnati ke yi, ya kuma kara da cewa hatta likitan dake duba malamin nasu ya ce yana cikin mawuyacin hali domin kuwa baya iya aiwatar da komi.
Ya kara da cewa suna mika koken su musamman ga shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi kokarin sakin malamin nasu domin ya sami ganin likitocin da suka kamata su duba lafiyar sa. Ya ce jama’ar su basa neman tada zaune tsaye, doming a kungiyoyin tsageran Niger Delta na abinda suka ga dama, ga kungiyar boko haran duk ana neman sasanci da su, dan haka suna kira ga gwamnati ta sakar masu malamin su.
Zanga zanagar nemo sako shugaban mabiya shi’a a Najeriya ta dauki dogon sahu a jihar ta Kaduna, inda bayan an kai kokuwar birnin, daya daga cikin shugabannin masu zanga zangar Malam Abdulhamid Garba ya yi wa magoya bayan Zak Zakyn bayanin cewa wajibi ne a sako masu shugaban su, da kuma sauran ‘yan uwansu dake tsare, ya ce wannan sako ya kamata ya shiga kunnuwansu domin gaggauta sako malamin nasu.
Daga karshe ya bukaci gwamnatin Najeriya ta hukunta wadanda suka ciwa sauran ‘yan uwansu zarafi domin a cewar sa, hakan shine zai kawo zaman lafiya a kasar, kuma ya kara da cewa wannan fitowa da suka yi somin tab ice kawai.
ASP Aliyu Muhammad shine kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya bayyana cewa a kowane lokaci a shirye suke domin su tabbatar da tsaro da kuma tabbatar da ganin al’umma ta bi doka da oda, dan haka jami’an sun bisu zuwa duk wuraren da suka gudanar da zanga zangar domin kare al’ummar gari da kuma su kansu masu gudanar da zanga zangar domin kaucewa rashin jituwa ko wani abu makamancin haka.
Domin Karin bayani ga rahoton Isa Lawal Ikara.