Gulen dai na zaune ne a jahar Pennsylvania da ke gabashin Amurka, kuma Turkiyya na bukatar a mika ma ta shi ba tare da bata lokaci ba, ta na mai zarginsa da shirya juyin mulkin nan na watan jiya wanda bai yi nasara ba -- zargin da Malamin ya karyata.
Biden ya gana jiya Labara da Shugaban Turkiyya Raccep Tayyip Erdogan. Ya yi kokarin sanya Erdogan ya sassauto game da nuna rashin hakurinsa, ta wajen bayyana yadda kotunan Amurka kan bukaci kwararan hujjoji, kafin a mika ma wata kasa mutumin da ta ke zargi.
Ya ce masu gabatar da kara na bukatar su nuna ma alkali abubuwan ka iya zama dalilan aukuwar al'amari, kuma wani sa'in kotunan kan bi a hankali. Biden ya yi nuni da yiwuwar a tsige Shugaba Barack Obama, muddun ya ba da umurnin tasa keyar wani dan kasar waje ba tare bin cikakken ba'asi ba.
Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya ce muddun aka bata lokaci wajen tasa keyar Gulen zuwa Turkiyya, to dangantakar Amurka da Turkiyya fa za ta yi tsami.
Biden ya ce ya fahinci bacin ran Turkiyya, ya kuma kara da cewa Amurka fa ba ta da wata niyya ta kare duk wani mutumin da ya yi wani abin da ka iya lahani ga kawarta.
v