Cikin wata sanarwa da babban Daraktan kamfanin NNPC Mele Kyari ya fitar a Abuja, ya bayyana cewa yunkurin hakan na zuwa ne bisa umarnin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar.
Shugaba Buhari ya umarci ma’aikatar albarkatun man fetur da kamfanin na NNPC da kuma hukumar tsaro ta EFCC da ma sauran hukumomin tsaro a kasar, da su yi dukan abin da ya kamata wajen dakatar da matsalar fasa bututun mai, sata da fasa kwaurin albarkatun mai da ake yawan samu a kasar.
Mele Gyari ya kwatanta matsalar a matsayin wata babbar barazana ga tattalin arzikin kasa wanda ya hana yan’Najeriya cin moriyar tallafin man fetur a kasar.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki a dukkan ma’aikatu da su hada hannu tare da kamfanin wajen tabbatar da cewa an wadatar da kasa da albarkatun mai da take bukata a kullum, wanda a halin yanzu ya rage daga lita miliyan 102 a watan Mayu zuwa lita miliyan 60.
Ko da yake dai Kyari ya jaddada cewa ba Najeriya kadai ke shanye dukkan man da ake samarwa ba.