Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Masana Shari’a Suka Ce Kan Hukuncin Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu

Masana shari'ar sun ce mutane da dama sun yi wa wannan hukunci mummunar fahimta domin shari'ar tana da fuskoki biyu.

ABUJA, NIGERIA - Saboda haka kotun ta wanke shi tare da ba da umarnin a sallame shi nan take. Kotun ta yanke hukuncin karar da Nnamdi Kanu ya shigar ta hannun lauyansa, Ifeanyi Ejiofor don bukatar soke sauran caji 7 da a ke yi ma sa ciki da tuhumar ta’addanci.

Masu shari’a a kotun karkashin Jostis Hannatu sun yanke hukuncin matakin da gwamnati ta bi wajen taso keyar Kanu ya sabawa dokokin cikin gida da ma na waje a bangaren maido da mai laifi kasar da a ke tuhumarsa.

Wannan hukuncin kotun dai ya zama wani tubali don ci gaba da zaman shari’ar Nnamdi Kanu in ji lauyansa, Ifeanyi Ejiofor.

Ko mene ne hukuncin kotun daukaka karar ke nufi la’akari da labarai daban-daban da suka mamaye kafafen sadarwa da ake yi wa hukuncin fassara daban-daban.

"Da yawa daga cikin masana, lauyoyi, 'yan jarida sun yi wa abin mummunar fahimta, da yawa yadda ake yayata abin ba haka yake ba. Wannan shari'a da aka yi a kotun daukaka kara, shari'a ce wacce wadda take, ta shafi hanyar da aka bi aka kawo shi daga kasar Kenya, ita ce kawai abin da kotun nan ta yi magana." In ji fitaccen lauya Barista Mainasara Kogo da bayani.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan lamarin inda shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Alhaji Nastura Ashir Sahriff, ya ce ga mai hankali, wannan hukuncin kotun da sake, don la’akari da yadda Nnamdi Kanu ya harzuka mambobin kungiyarsa ta IPOB su yi ta kashe mutane da ba su ji ba su gani ba.

A matsayin martani ga mabanbantan ra’ayoyin ‘yan kasar kan hukuncin kotun na ranar Alhamis da ya sallami Kanu, ministan shari’a Abubakar Malami, ta bakin mai magana da yawunsa, Dakta Umar Jibril Gwandu, ya ce ya kamata jama’a su fahimci cewa shari’ar Nnamdi Kanu na da fuskoki guda biyu da suka hada da tuhume-tuhumen da a ke masa kafin ya arce daga kasar da wadanda a ke masa a lokaci arcewarsa da kuma bayan arcewarsa.

Idan Ana iya tunawa, a shekarar 2017 ne Nnamdi Kanu ya fara fuskantar shari’a a bisa zarginsa da aikata laifuffuka masu nasaba da cin amanar kasa har wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bayar da belinsa a watan Afrilun shekarar daga bisani ya tsallake belin biyo bayan bijirewa dukkan sharuddan da kotu ta gindaya.

A watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta sami nasarar sake kama Nnamdi Kanu tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka a kasar Kenya a lokacin da ya ke neman goyon bayan kasashen waje domin tabbatar da samun kasar Biyafara.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Abin Da Masana Shari’a Suka Ce Kan Hukuncin Nnamdi Kanu
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

XS
SM
MD
LG