Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanai akan shugaban 'yan aware Nmamdi Kanu na IPOB, cewa ba za a sake shi haka kawai ba sai ya kare kansa.
Amma tsohon shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekwerenmadu ya ce za a iya warware matsalar a siyasance, sai dai kwararru a fannin siyasa na ganin abin da kamar wuya.
Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekwerenmadu ya ce duk da bayanai masu karfi da shugaban Buhari ya fitar a kan Nnamdi Kanu, har yanzu da shi da 'yan yankin Kudu Maso Gabas inda Kanu ya fito suna ci gaba da neman hanyar warware rikicin siyasar da ya shafi Shugaban Masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
Kanu na fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi ta'addanci, kashe-kashen mutane da cin amanar kasa, abin da ya sa ake garkame da shi a wurin jami'án tsaro na farin kaya.
Baya ga kiraye-kiraye da wasu shugabanin Igbo suka yi a bara lokacin da suka kai wa shugaba Buhari ziyara, Ekwerenmadu ya ba da misalin irin tuntubar da 'yan asalin Igbo suka yi a lokacin da aka kama tsohon shugaban MASSOB Ralph Uwazuruike, har aka kai ga sako shi.
Amma kwararre a fannin zamantakewar dan Adam kuma Malami a jami'ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya ce akwai banbanci tsakanin Uwazuruike da Nnamdi Kanu.
Shi ma kwararre a fannin siyasar da diflomasiyar kasa da kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi nazari akan batun Nnamdi Kanu kamar inda ya ce akwai babanci tsakaninsu saboda shi Uwazuruike hada kan yan kasuwa ya ke yi, yana sayar musu da akidar Biafara, yana karban changinsa yana ajiyewa, Kanu kuwa kawar da Uwazuruike ya yi, ya mayar da akidar ta kasha-kashe.
A yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido, su ga irin tasirin da siyasa za ta yi a wannan magana ta Nnamdi Kanu shugaban yan aware masu neman a basu kasar Biafra.