Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sake Watsi Da Bukatar Neman Belin Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Hoto: Channels TV)
Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Hoto: Channels TV)

A yau Talata wata kotun Tarayya a Abuja ta ki amincewa da bukatar neman beli ga shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB, Nnamdi Kanu da ke tsare.

An shigar da karan ne yayin da ake jiran hukuncin da kotun za ta yanke masa a kan laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya take zarginsa da aikatawa.

Kanu wanda yake fuskantar tuhume-tuhume guda bakwai, a cikin karan da ya shigar wa kotu ta hannun rukunin lauyoyinsa a jagorancin Chief Mike Ozekhom, ya kalubalanci soke belin da kotu ta bashi a baya.

Ya roki kotun da ta yi watsi da umarnin da ta bayar a ranar 28 ga Maris, 2019, wanda ba wai kawai ta bayar da sammacin kama shi ba, har ma ta baiwa Gwamnatin Tarayya damar gurfanar da shi a lokacin da ba ya nan.

Shugaban kungiyar ta IPOB ya shaida wa kotun cewa sabanin zargin da Gwamnatin Tarayya ta yi na cewa ya tsallake beli, ya gudu ne domin tsira da ransa bayan da sojoji suka mamaye garinsa da ke Afaraukwu Ibeku a Umuahia a jihar Abia, lamarin da ya ce ya yi sanadin mutuwar mutane 28.

A yayin da yake ikirarin cewa an yi masa rashin adalci na kin sauraron shi kafin a soke belinsa, Kanu ya yi nuni da wasu abubuwa guda takwas da suka hada da hotuna, da kuma wata takardar rantsuwa da ya yi daga Isra’ila, bayan ya gudu daga kasar.

A halin da ake ciki kuma, yayin da ta yi watsi da bukatar belin, mai shari’a Binta Nyako a ranar Talata, ta ce ba ta gamsu da dalilin da shugaban kungiyar ta IPOB ya bayar na rashin gurfana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar sa ba.

XS
SM
MD
LG