Kotun daukaka kara a Abuja, babban birnin Najeriya, ta wanke shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafra Nnamdi Kanu a ranar Alhamis a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
A watan Yulin bara aka tuso keyar Kanu daga Kenya bayan da ya tsere a shekarar 2017 a lokacin yana karkashin beli.
Ana tuhumar Kanu da laifuka 15 da suka danganci cin amanar kasa da ta’addanci, wadanda ake zargin ya aikata yayin da yake fafutukar kafa kasar Biafra.
Sai dai kotun daukaka karar mai alkalai uku, ta ce babbar kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraren karar ta Kanu.
Kazalika kotun ta ce ba a bayyana lokaci, kwanan wata da inda Kanu ya aikata laifukan 15 da ake zargin ya aikata ba.
Kungiyar ‘yan aware ta IPOB wacce Kanu ke jagoranta a kudu maso gabashin Najeriya, ta jima tana fafutukar neman ballewa daga kasar.
Sai dai gwamnatin tarayya ta zarge shi da amfani da kungiyar wajen ta da husumar da ke salwantar da rayukan jama’a.