Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tare da hadin gwiwa da hukumar kula da yawan al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya ne suka jagoranci kaddamar da wannan shiri.
Yawan korafe korafe ne yasa hukumar dake kula da yawan jama’a ta MDD daukar matakin yin bincike inda suka gano cewa kashi 60 na ‘yan mata ne ake yiwa aure tun basu kai shekaru 18 ba, a yawancin kasashen nahiyar Afirka.
Najeriya dai na daga cikin jerin kasashen da suka sa hannu akan dokar ‘yancin yara na shekara ta 2003, inda aka kayyade shekaru 18 a matsayin shekarar da yarinya sai ta kai kafin ayi mata aure.
Ministan kula da ayyukan ma’aikatar mata da lamuran al’umma ta Najeriya, Hajiya Aisha Alhassan, wacce ta shiga wannan yunkuri a madadin mata, tace idan za a aurar da yara a bari akalla tayi wayo ta kai shekaru 18, ta yadda zata iya daukar ciki ta kuma haihu lafiya.
An dade ana kokarin kayyade shekarun aurar da yara mata musamman a shiyoyin Arewacin Najeriya, amma kuma har yanzu ba a sami nasarar yin hakan ba.
Hukumar kula da yawan al’umma ta MDD da kuma wasu kungiyoyi na kasashen waje da na cikin gida masu yawa ne suka ja ragamar kaddamar da wannan shiri. Kasashen 15 ne suka riga suka kaddamar da irin wannan kamfen din a nahiyar Afirka.
Domin karin bayani.