Darakta a hukumar kula da gidajen talabija ta kasa Dr, Armstrong Idachaba ya bayyana haka bayan taron karawa juna sani kan fasahar zamani da ta shiryawa kafofin yada labarai na jihohin Adamawa, Bauchi, Yobe, Borno,Gombe da Taraba a Yola fadar jihar Adamawa.
Wasu daga cikin mahalarta bitar sun nuna fargabar sauyin na iya raba da dama daga cikin masu tsara shirin radiyo da talabijan na iya rasa aikinsu sakamakon maye gurbinsu da na’urori masu kwakwalwa kamar yadda Dr, Abba Tahir tsohon shugaban gidan radiyo na jihar Adamawa ya shaida a hirarsa da Muryar Amurka.
A daya bangaren wasu na ganin sabanin haka shirin zai kara habaka sana’ar tsara shirin gidan radiyo da talabijan da samar da karin ayukan yi inji darakta a ma’aikatar yada labarai na jihar Yobe Mal. Mohammed Abubakar Babe.
Kawo yanzu sau biyu ke nan ana dage anfani da shirin, sai dai da alamun shirin gwajin da aka soma a jihar Filato ya soma cimma nasara.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.