Bayan sun kammala taronsu na darikar Tijjaniya da suka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa, Shaikh Dahiru Bauchi, daya daga cikin shugabannin addinin musulunci a Najeriya yana ganin dole ne gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ta magance matsalar kuncin rayuwa da ake fama da ita a kasar yanzu.
Shaikh Dahiru Bauchi yace a ji tausayin mutane saboda suna cikin wahala musamman wahalar abinci. Yace a tausaya masu a samu hanyar da za'a tare abincin da aka noma cikin gida domin kada a yi waje dashi. Wanda ma yake waje a shigo dashi a kara kan na gida.
Malamin ya ci gaba da cewa a dubi duk abubuwan da suka dami mutane a yi masu maganinsu kama daga gwamnatin tarayya zuwa na jihohi da na kananan hukumomi. A tausayawa jama'a.
Yayinda ya juwa kan takunsakan da ake samu da 'yan kungiyar Shi'a da hukumomin kasar, Shaikh Bauchi yace akwai abun dubawa. A hada kai tsakanin musulmai da makwaftansu da ba musulmai ba domin a zauna lafiya. Kowa yayi abun dake gabansa tunda kasar ta ba kowa damar yayi addinin da yake so. Yace to kowa yayi nasa kada a tsangwameshi, shi kuma kada ya tsangwami kowa.
Yace kodayake tashin hankali a arewa maso gabas yayi sauki amma ta wajen Zamfara sai karuwa yake yi. Suna rokon Allah ya kawo sauki.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.