Babban jakadan Amurka, Mr. John Bray, shine ya sanar da hakan a birnin Lagos a wajen wani taron bita akan akan lafiya, albarkacin ranar bikin yaki da cutar HIV. A cewar jakadan gwamnatin Amurka ta samar da wannan kudi ne karkashin wani shiri na shugaban kasar Amurka da aka fara a shekara ta 2004.
Jakada Bray, yace Amurka ta damu matuka na ganin cewa an kawo karshen yaduwar cutar HIV mai karya garkuwar jiki a nahiyar Afirka baki daya. Kuma a matsayin Najeriya na babbar kasa a Afirka yasa Amurka tafi mayar da hankali a kasar.
A cewar hukumomi a Najeriya yanzu haka kwayar cutar ta HIV na ci gaba da raguwa. Binciken hukumar dake kula da cutar HIV a jahar Lagos, LSACA, ya nuna cewa kimanin mata masu juna biyu 1702 suka kamu da cutar, yayin da kuma ake kula da su. Haka kuma kimanin jarirai 1143 ne aka haifesu da cutar HIV a cewar kwamishinan lafiya na jahar Lagos.
Kamar yadda kwamishinan yayi bayani kimanin mutane 5492 ke dauke da wannan cuta ke karbar magungunan rage karfin cutar.
Gwamnatin jihar Lagos dai na gudanar da bita ta ilimantarwa a makarantun sakandare kimanin 250 dake fadin jahar.
A cewar babban Daraktan hukumar kula da yaduwar cutar HIV a Najeriya, Dakta Aliyu Idris, yanzu haka an samu raguwar masu kamuwa da cutar a fadin kasar.
Ranar 1 ga watan Disambar kowacce shekara ranace da hukumar Lafiya ta MDD ta ware a matsayin ranar bita da ilimantar da jama’a game da illar cutar HIV/AIDS mai karya garkuwar jikin bil Adama.
Domin karin bayani.